Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti{a.s} - ABNA - Rahotanni sun ce mayakan 'yan Tigray da ke gwabza fada da dakarun gwamnatin Habasha sun fara janyewa daga garuruwa da ke makwabtaka da yankin arewacin kasar da a baya suke karkashin ikonsu.
Mai magana da yawun yan tawayen na TPLF Getachew Reda ya shi ma ya tabatar da hakan.
Dama tun a baya daga cikin sharudan da gwamnati ta gindaya musu da za su kai ga tattaunawa sun hada da barin wadannan garuruwan.
Ana fatan wannan mataki na 'yan tawayen ya kai ga hawa teburin sulhu da zai kawo karshen rikicin da aka kwashe shekara guda ana yin shi wanda ya yi sanadiyar rayukan mutane da dama da raba wasu da matsugunansu.
A nata bangare Amurka ta yi fatan matakin mayakan na yankin Tigray zai bude kofar tattaunawa ta hanyar diflomatsiyya.
342/